Labarai
Gwamnatin Najeriya za ta kara karfafa tsaro a kan iyakokin kasar
Gwamnatin tarayya ta ce za ta kara karfafa tsaro a kan iyakokin kasar nan da kasashe 7 na tsandauri da kuma na ruwa domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Najeriya.
Darakta janar na hukumar kula da iyakoki ta kasa da ke karkashin fadar shugaban kasa Adamu Agaji da takawaransa mai kula da iyakokin ketare Mustapha Ribadu ne suka bayyana hakan a taron bikin ranar iyakoki ta Afirka karo na 11 da aka gudanar a birnin Addis Ababa na kasar Ethiopia.
Sun kara da cewa za su yi aikin ne da hadin gwiwar jami’an tsaro domin samun nasarar kawar da aikata miyagun laifuka a Najeriya.
Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da zargi ya yi karfi kan cewa wasu bata-gari daga kasashen ketare na shigowa Najeriya suna aikata ta‘addanci suna kashe mutane da ma sauran laifuffuka.
You must be logged in to post a comment Login