Connect with us

Labarai

Gwamnatin Neja ta bukaci wanda sukayi gini akan hanyar ruwa da su tashi

Published

on

Gwamnatin jihar Neja ta bukaci mazauna yankunan da suka gina gidaje a kan magudanan ruwa da su yi gaggawar tashi don kaucewa ambaliyar ruwa.

Mataimakin gwamnan jihar Yakubu Garba ne ya ba da umarnin a jiya Laraba yayin ziyarar duba wasu yankuna da ambaliyar ruwa ta shafa, biyo bayan mamakon ruwan sama da aka a kwanakin baya a jihar.

Ya kuma umarci hukumar raya birane ta jihar da hukumar bada agajin gaggawa NSEMA da hukumar kare muhalli NISEPA da su wayar da kan jama’ar da ke zaune a magudanan ruwan kan illar da ke tattare hakan.

Rahoton: Abdulkadir Yusuf Gwarzo

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!