Ƙetare
Gwamnatin Saudiyya na shirin fara cin tarar masu aikata rashin ɗa’a

Gwamnatin kasar Saudiyya ta sanar da cewa za ta fara kakaba tarar kuɗi kan duk wanda aka samu da aikata ayyukan da suka saba da ɗa’a a cikin al’umma, musamman a lokutan ibada kamar sallah.
Hukumomin kasar sun bayyana cewa an ɗauki wannan mataki ne domin kare mutunci da tabbatar da tsaro da kuma samar da zaman lafiya ga jama’a.
A cewar sanarwar, duk wanda ya aikata laifin da ya shafi karya dokokin ɗabi’a ko rashin ladabi a wuraren ibada zai fuskanci hukuncin tara, kodayake ba a bayyana takamaiman adadin kuɗin ba.
Hukumomin sun kara da cewa matakin ya zama wajibi ne ganin yadda dubban al’umma daga sassa daban-daban na duniya ke taruwa a Saudiyya a lokutan ibada, lamarin da ke bukatar ƙarin tsaurara matakan tsaro da ladabi.
You must be logged in to post a comment Login