Labarai
Gwamnatin Shugaba Tinubu na shirin ciyo bashin fiye da Tiriliyan 17

Gwamnatin Tarayya ta ƙuduri aniyar ciyo bashin Naira sama da Naira tiriliyan 17, domin cike gibi a kasafin kuɗin shekarar 2026, saboda karancin kudaden shiga idan aka kwatanta da bukatun kashe kuɗin da ke cikin kasafin.
Sabbin bayanan da Ma’aikatar Tsare-Tsaren Tattalin Arziki ta fitar sun nuna cewa gibin kasafi zai tashi zuwa Tirilian 20 da digo 12.
A taron tattaunawa kan batun bashi a da ya gudana a birnin tarayya Abuja, kungiyoyin farar hula sun soki wannan batu, abin da suka kira da yawan ciyo bashin da ba ya samar da cigaba ga al’umma.
Kazalika masanan sun jaddada cewa yawan ciyo bashin na iya jefa yan Najeriya cikin mummunan yanayi.
You must be logged in to post a comment Login