Labarai
Gwamnatin Sokoto za ta raba wa jami’an tsaro babura 1,000 don yaki da ƴan bindiga

Gwamnatin Jihar Sokoto ta amince da kashe sama da Naira biliyan 1 domin sayen babura ƙirar Bajaj guda 1,000 da za a raba wa hukumomin tsaro a jihar, domin ƙarfafa yaƙi da ƴan bindiga.
A cewar daraktan janar na yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gidan gwamnatin Sokoto, Abubakar Bawa, an amince da wannan buƙatar ne a majalisar zartarwar jihar.
Abubakar Bawa ya ce, Sayen babura guda 1,000 na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ta ɗauka domin ƙara wa jami’an tsaro kayan aiki da za su taimaka wajen gudanar da ayyukansu a wuraren da matsalar ƴanbindiga ta fi ƙamari.”
Ya ƙara da cewa sayen baburan zai kasance ƙarin tallafi ne ga motocin yaƙi masu sulke guda 62 da gwamnatin jihar ta saya kwanan nan, waɗanda darajarsu ta kai Naira biliyan 27.
You must be logged in to post a comment Login