Connect with us

Labarai

Yan Zambiya na kada kuri’a a zaɓen shugaban ƙasa da ƴan majalisar dokoki

Published

on

Al’ummar Zambiya na gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisar dokokin ƙasar.

 

Ana kallon zaɓen a matsayin ma’aunin gwajin ingancin dimokuraɗiyya a ƙasar mai tarihin ‘ɗorewar tsarin dimokuraɗiyya a Afrika.

 

Shugaban ƙasar Hakainde Hichilemana wanda ke neman wa’adi na biyu na da farin jini sakamakon rawar da ya taka lokacin da ƙasar ke fama da matsin tattalin arziki.

 

Ana ganin za a fafata ne tsakanin shugaban ƙasar da jagoran adawa Brian Mundibile wanda magoya bayan tsohon shugaban ƙasar Edgar Lungu ke mara wa baya.

 

Ɗan takarar shugaban ƙasa dai na buƙatar sama da kashi 50 na ƙuri’u kafin ya yi nasara.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!