Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya da wasu kasashen Afrika 22 sun dauke gabarar habbaka sufurin jiragen sama
Gwamnatin tarayya tare da wasu gwamnatocin kasashen Afirka 22 sun dauki gabarar samar da wata doka da zata taimaka wajen harkokin inganta sufurin jiragen sama, duk da nufin samar da yanayin kasuwanci mai kyawu ga masu hada-hadar jiragen sama na kasuwanci.
An kaddamar da kamfanin na bai daya da zai inganta harkokin sufurin jiragen sama a Afirka ne yayin babban taron kungiyar hadin kan kasashen Afirka ta AU wanda aka gudanar a Addis Ababa na kasar Habasha.
Rahotanni sun bayyana cewa jirage daga kasashen ashirin da uku zasu iya fadada ayyukan su zuwa sauran kasashen da suka amince da shirin.
A cewar hukumar lura da harkokin jiragen sama ta kasa da kasa idan har kasashen afirka goma sha biyu suka bullo da makamancin wannan shiri, shakka babu za’a samu guraben aikin yi kimanin dubu dari da hamsin da biyar, tare da samar da kudaden shiga sama da dala biliyan guda duk shekara a kasashen.
Hukumar ta kuma yi hasashen cewa za’a samu karuwar zirga-zirgar fasinjojin a Nijeriya daga dubu dari bakwai da saba’in da hudu zuwa miliyan guda da dubu dari da saba’in da daya cikin wata guda, idan har aka samar da sabon tsarin.