Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙara yawan ɗaliban da ake ɗauka a makarantun koyon aikin jinya

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta ƙara yawan ɗaliban da ake ɗauka a makarantun koyon aikin jinya daga dubu Ashirin zuwa Hamsin a duk shekara.

A cewar ta ta yi hakan ne domin magance ƙarancin ma’aikatan lafiya tare da ƙarfafa fannin kiwon lafiya a ƙasar nan.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa da manema labarai da ya yi a Abuja.

Ya kuma ce wannan na daga cikin sauye-sauyen da gwamnati ke aiwatarwa domin samar da ƙwararrun ma’aikatan da za su taimaka wajen cimma burin gwamnati.

A cewarsa, gwamnati na ci gaba da zuba jari wajen bunƙasa ilimi da ƙwarewar matasa, musamman a muhimman fannoni da ƙasar nan ke buƙata.

Ya ce baya ga aikin jinya, an kuma ƙara yawan ɗaliban da ake ɗauka a fannonin likitanci, harhaɗa magunguna da likitan haƙora, domin rage ƙarancin ƙwararrun ma’aikatan lafiya a Najeriya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!