Labarai
Kaduna: Mutane 30 sun rasu sakamakon harin masu dauke da makamai a kauyen Naridon

Akalla mutum 30 sun rasa rayukansu a wani hari da wasu dauke da makamai suka kai kauyen Naridon da ke gundumar Kamaru a karamar hukumar Kauru ta jihar Kaduna.
Rahotanni sun ce maharan sun kai harin ne da misalin karfe 1:00 na dare, inda suka rika harbin kan main uwa da wabi.
Kungiyar Amnesty International ta ce maharan sun bi wasu da suka gudu zuwa cikin daji tare da kashe su, yayin da ake ci gaba da gano karin gawarwaki a gidaje da gonaki.
Kungiyar ta zargi gwamnati da gaza kare rayuka tare da bayyana cewa hare-haren makamantan wannan sun sha faruwa a yankin Kudancin Kaduna. Zuwa lokacin wallafa rahoton, rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance kan harin ba.
You must be logged in to post a comment Login