Labarai
Gwamnatin Kano za ta taimaka wa duk dan shaye-shayen da ya tuba- Barista Muhyi

Shugaban Kwamitin yaƙi da shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safararsu, na jihar Kano Barista Muhuyi Magaji Rimingado, ya buƙaci masu shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da su tuba, yana mai tabbatar da cewa Gwamnatin Jihar Kano za ta tallafa wa duk wanda ya daina shaye-shaye ta hanyar gyaran hali, mayar da shi cikin al’umma da kuma ba shi damar dogaro da kai.
Barista Muhyi ya bayyana hakan ne a wani taro da ya gudana na zaman lafiya a unguwar Dorayi da ke karamar hukumar Gwale a nan Kano.
In da ya ce gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta himmatu wajen yaƙi da shaye-shaye. Sai dai ya yi gargaɗin cewa duk wanda aka samu yana ajiye ko safarar miyagun ƙwayoyi, ko kuma aka tabbatar ana amfani da gidansa wajen irin waɗannan ayyuka, zai fuskanci hukuncin doka ciki har da soke takardar mallakar gidan.
Ya kuma jaddada cewa kwamitin ba zai lamunci tsoma bakin ‘yan siyasa ko masu faɗa a ji wajen hana gudanar ayyukansa ba.
You must be logged in to post a comment Login