ilimi
Gwamnatin Tarayya ta amince da sabbin jami’o’i 9

Gwamnatin tarayya ta amince da kafa sabbin jami’o’i masu zaman kansu guda tara.
Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa, ne ya sanar da hakan a jiya Laraba, yayin da yake zantawa da manema labarai a fadar shugaban ƙasa, bayan taron majalisar zartarswa ta ƙasa da shugaba Bola Tinubu ya jagoranta a birnin tarayya Abuja.
Ya ce, jami’o’in da aka amince da su sun haɗa da:
Jami’ar Tazkiyah da ke jihar Kaduna
Jami’ar Leadership da ke babbar birinin tarayya, Abuja
Jami’ar Jimoh Babalola a jihar Kwara
Jami’ar Bridget, Mbaise a jihar Imo
Jami’ar Greenland da ke jihar Jigawa
Jami’ar JEFAP a jihar Neja
Jami’ar Azione Verde da ke jihar Imo
Jami’ar Unique Open a Jihar Legas
Jami’ar American Open da ke Jihar Ogun
A cewar Ministan gwamnatin Tinubu ta gaji buƙatu 551 na kafa sababbin jami’o’i, inda aka saka tsauraran ka’idojin tantancewa kafin amincewa da su.
Alausa ya ce da dama daga cikin jami’o’in da aka amince da su suna jiran samun izinin aiki sama da shekaru shida, duk da cewa masu hannun jari sun riga sun gina harabar makaranta tare da zuba biliyoyin naira a ciki.
You must be logged in to post a comment Login