Labarai
Gwamnatin tarayya ta bada umarnin tura dakarun soji don fatatakar yan bindiga

Gwamnatin tarayya ta jaddada umarninta ga rundunar soji kan ba za dakaru cikin dazuka tare da domin ci gaba da yin farautar yan ta’adda da suka addabi al’umma musamman a yankunan Arewa.
Karamin ministan tsaro kana tsohon gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ne ya bayyana hakan a wata hira ta musamman da manema labarai.
In da ya ce tuni rundunar sojin Najeriyar suka fara aiwatar da wannan umarni na shugaban kasa Tinubu.
Da ya ke tsokaci kan halin rashin tsaro da jiharsa ta zamfara ke ciki, Matawalle ya zargi gwamanan jihar mai ci Dauda Lawal da kin hada hannu da shi wajen shawo kan matsalar, Bayan da ya ce gwamnan ya tsallakeshi tare da zuwa wurin ministan tsaro kuma tsohon gwaman jigawa Badaru Abubakar.
You must be logged in to post a comment Login