Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta biya ma’aikatan rusashen kamfanin jirgin saman Najeriya kudaden sallama
Gwamantin tarayya ta fito da sunayen mutane 114 wadanda tsoffin ma’ikata rusashen kamfanin jirgin saman na kasa Nigerian airways ne, da aka biyasu kudaden sallama daga aka aiki har sau biyu, kuma suka ja bakin su suka yi shiru.
Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar ma’aikatan harkokin sufirin jiragen sama ta kasa AUGA Lukuman Animashauna ya fitar a jiya.
Ta cikin sanarwar kungiyar ta ce gwamnatin tarayya ta sanar da ita cewar ta lurta da an biya wasu ma’aikatan har sau biyu amma sun tsuke bakunan su sun yi shiru.
Sanarwar ta kuma bukaci dukkanin mutanen da aka yiwa aringizon, da su ziyarci bankunan su a yau Litinin domin gyara matsalolin nasu, ta yadda za a baiwa wadanda basu karba ba damar samun nasu kudaden.
Sanarwar ta kuma yi gargadin cewar duk wanda ya ki halartar bankin nasa domin gyara matsalar sa a yau litinin to ba shakka za a cire shi daga cikin wadanda za su ci ga ba da amfana dafanshon su baki daya.