Gwamnatin Tarayya ta ce ƙasashe 65 daga cikin 69 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wa jakadu sun amince da karɓar su, abin da ya kai kashi 97 cikin 100 na dukkan nade-naden.
Ma’aikatar Harkokin Wajen Najeriya ta bayyana cewa ƙasashe biyu ne kaɗai suka rage ba su kammala bayar da amincewarsu (agrément) ga jakadun da aka tura musu ba.
A cewar ma’aikatar, jakadan da aka nufa da tura shi ƙasar Togo ya ƙi karɓar nadin, yayin da jakadan da aka tura Aljeriya ya rasu a watan Afrilun 2026.
Sanarwar ta ƙara da cewa yawancin jakadun da aka naɗa sun riga sun isa ƙasashen da aka tura su, inda suka gabatar da takardun shaidar aikinsu ga shugabannin ƙasashen da za su yi aiki, tare da fara gudanar da ayyukansu na wakiltar Najeriya.
Tun a watan Maris na 2026 ne Shugaba Tinubu ya amince da tura jakadu 69 zuwa ƙasashe daban-daban da kuma ofisoshin Majalisar Ɗinkin Duniya, bayan Majalisar Dattawa ta tabbatar da su.
You must be logged in to post a comment Login