Connect with us

Labarai

Gwamnan Kogi Ahmed Usman Ododo ya yaye jami’an tsaron dazuka 530

Published

on

Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya yaye jami’an tsaron dazuka 530.

 

Wannan na cikin sanarwar da Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar, Kingsley Femi Fanwo, ya fitar a jiya Asabar

Sanarwar ta ce an gudanar da bikin yaye rukuni na farko na jami’an tsaron dazuka a Muhammadu Buhari Civic Centre da ke Lokoja.

Ya ce mutane 539 ne suka fara horaswar ta makonni takwas, inda 530 suka kammala domin fara aiki.

Sanarwar ta ce gwamnan ya sake jaddada aniyar gwamnatinsa ta ci gaba da samar da kayan aiki da tallafin da ake buƙata domin ƙarfafa hukumomin tsaro, tare da kira ga mazauna jihar su riƙa ba jami’an tsaro sahihan bayanan da za su taimaka wajen inganta tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!