Labarai
Kwamitin yaƙi da faɗan daba da miyagun ƙwayoyi ya kai samame wasu wurare

Kwamitin karta-kwana na yaƙi da faɗan daba da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi na Jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin shugabansa, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya kai ziyarar duba wasu manyan wuraren da ake zargin ana gudanar da hada-hadar miyagun ƙwayoyi a cikin Birnin Kano.
Wuraren da kwamitin ya ziyarta sun haɗa da Rekwa, Filin Mahaha, Ɗan’agundi, Kwarin Dala da kuma Filin Sabuwar Kofa.
Ziyarar na daga cikin matakan da kwamitin ke ɗauka domin ƙara sa ido tare da ƙarfafa yaƙi da masu ta’ammali da safarar miyagun ƙwayoyi, da kuma magance matsalar faɗan daba da sauran ayyukan da ke barazana ga tsaro a faɗin jihar.
Da yake ƙarin bayani ga Freedom Radio, shugaban kwamitin, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, ya ce sun fara samun nasarori a ƙoƙarin da suke yi, yana mai jaddada cewa kwamitin zai ci gaba da irin waɗannan ziyarce-ziyarcen domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login