Labarai
Gwamnatin tarayya ta ce bata da lokacin tattauna batun zaben 2019
Gwamnatin tarayya ta ce ba ta da lokacin tattauna batun zaben shekarar 2019 a wannan lokaci da take kokarin cika alkawuran da ta daukar wa al’ummar kasar nan.
Gwamnatin na mayar da martani ne ga wasikar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban kasa Muhammadu Buhari abaya-bayan nan ya na mai shawartar sa kan tsayawa takara a zaben shekarar 2019.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammed ya fitar jiya a Abuja.
Sanarwar ta ce shugaba Buhari ba yi da lokaci da zai tsaya yana tattauna zaben shekarar 2019 abin da ke gaban sa a yanzu shine cika alkawuran da ya daukar wa al’ummar kasar nan yayin yakin neman zaben shekarar 2015.
Abaya-bayan nan ne dai tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya rubuta wata wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari yana mai shawartar sa da cewa ka da ya tsaya takara a yayin zaben shugaban kasa da za a yi a shekarar badi.