Labarai
Gwamnatin tarayya ta ce tana dab da kammala aikin Solar a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano

Gwamnatin tarayya ta ce nan da watanni uku masu zuwa za ta kammala aikin wuta mai amfani da hasken rana a Asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano domin tsayar musu da wuta ta tsawon awanni ashirin da hudu ba tare da ɗaukewa ba, domin kulawa da lafiyar al’umma.
Shugaban hukumar makamashi na ƙasar nan Dakta Abdullahi Mustapha ne ya bayyana hakan a yau yayin ƙaddamar da fara aikin wutar mai anfani da hasken rana a asibitin koyarwa na Malam Aminu kano wanda shugaban kwamitin shirye shiryen kasafin kuɗi na majalisar tarayya kuma ɗan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Bichi Abubakar Kabir Bichi ya samar.
A nasa jawabin shugaban kwamitin shirye shiryen kasafin kuɗi na majalisar tarayya kuma ɗan majalisa mai wakiltar Bichi Abubakar Kabir Bichi da ya assasa aikin yace ganin irin halin da asibitin yake ciki ya sanya shi wannan yunkuri na samar da kudi sama da biliyan sha shida domin samar musu da tsayayyiyar wuta a cikin asibitin.
Shugaban Asibitin na Malam Aminu Kano Farfesa Abdulrahman Abba Sheshe, a jawabin sa cikin harshen turanci ya godewa gwamnatin tarayya bisa yunkurin samar da wutar.
You must be logged in to post a comment Login