Labarai
Gwamnatin tarayya ta duƙufa wajen magance matsalolin tsaro- Ministan yaɗa Labarai

Gwamnatin tarayya ta bakin ministan yaɗa labarai da wayar da kan jama’a Modammed Idris, ta ce, ta duƙufa wajen magance matsalolin tsaron da ƙasar ke fuskanta, ta yadda ƴan ƙasar dama baƙi ƴan ƙasashen ketare za su kasance cikin tsaro a kowane yanki suke.
Jawabin Ministan, ya biyo bayan gargadin Ofishin kula da harkokin ƙasashe renon Ingila na Commonwealth da ya ce su guji yin balaguro zuwa jihohin Borno da Yobe da Adamawa da Gombe da Katsina da kuma Zamfara, saboda ƙaruwar tashe-tashen hankali da ta’addanci da kuma garkuwa da mutane.
A nata ɓangaren, gwamnatin jihar Kano ta bakin sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar Mustapha Muhammad, ta ce al’umma su ci gaba da gudanar da harkokinsu yadda suka saba, domin babu wata barzana kan wancan gargaɗi na gwamnatin Birtaniyya.
Haka nan itama gwamnatin jihar Borno, ta ce an samu gagarumar nasara wajen inganta lamuran tsaro a cikinta, da mai taimawa gwamna Babagana Zulum kan harkokin tsaro Janar Abdullahi Ishaq mai ritaya, ya ce ba za su ce komai game da kiran na Birtaniyya ba, gwamnatin tarayya ce za ta maida martani akai.
You must be logged in to post a comment Login