Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta fara bitar sabbin dokokin haraji

Published

on

Shugaba Tinubu

Gwamnatin Tarayya ta fara bitar sabbin dokokin haraji na tsawon makonni shida, domin gano gibin da ake samu wajen aiwatar da dokokin da kuma magance wasu matsalolin da suka kunno kai tun bayan fara aiki da su.

 

Ministan Kudi kuma mai kula da harkokin tattalin arziki, Taiwo Oyedele, ne ya bayyana hakan a Abuja, yayin kaddamar da wani karamin kwamiti na fasaha da zai taimaka wajen duba manufofin kasafin kudi da sauye-sauyen haraji.

 

Ya ce bitar za ta yi la’akari da damuwar da kungiyoyin ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki suka bayyana game da yadda ake aiwatar da sabbin dokokin.

 

Oyedele ya ce manufar bitar ba ita ce soke sauye-sauyen harajin da aka yi ba, sai dai gano wuraren da aka samun matsala da kuma yin gyare-gyaren da suka dace domin tsarin harajin ya zama mai saukin fahimta da aiwatarwa.

 

Ana sa ran kwamitin zai kammala aikinsa cikin makonni shida, sannan ya gabatar da shawarwarinsa, wadanda za su taimaka wajen tsara Finance Bill na shekarar 2027.

 

Sabbin dokokin harajin sun fara aiki ne daga ranar 1 ga Janairun shekarar 2026.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!