Labarai
Gwamnatin Kano za ta tallafawa makarantun kimiyya da kayan agaji

Gwamnatin Jihar Kano ta ce za ta ci gaba da tallafawa makarantun sakandare na kimiyya da fasaha da kayan aiki da na agaji, domin bunƙasa harkokin ilimi a fannin.
Sakataren Zartarwa na Hukumar Kula da Makarantun Kimiyya da Fasaha ta jihar, Farfesa Dahiru Sale Muhammad, ne ya bayyana hakan a yayin wani taron ƙaddamar da shirin rabon kayan kashe gobara da kayan wasanni ga makarantun.
Ya ce samar da irin waɗannan kayan na daga cikin matakan da ake ɗauka domin inganta yanayin koyarwa da koyo a makarantun kimiyya da fasaha na jihar.
A nasa jawabin, Haya Sufeto Janar na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Ibrahim Umar Muhammad, ya bayyana matakan da ya kamata a ɗauka domin rage haɗarin iftila’in gobara da kuma kare rayuka da dukiyoyi.
Ya kuma jaddada muhimmancin wayar da kan ɗalibai da ma’aikatan makarantu kan hanyoyin da za su taimaka wajen dakile gobara da kuma matakan gaggawa idan gobara ta tashi.
Wakilinmu, Akilu Musa Garba Diso, ya ruwaito cewa taron ya samu halartar wakilai daga makarantun sakandare na kimiyya da fasaha na jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login