Connect with us

Labarai

Tinubu ya bukaci a yi bincike kan mutuwar mutane 37 a Neja

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci a gudanar da cikakken bincike kan mutuwar mutane 37 da ake zargi da hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, wadanda suka mutu yayin da suke tsare a hannun rundunar Tsaron farar hula ta kasa NSCDC a minnan, Jihar Neja.

 

Mutanen dai an kama su ne a ranakun 15 da 16 ga Satumba, yayin wani samame da jami’an NSCDC suka gudanar a yankin M.I. Wushishi da Lukoto, da ke Minna.

 

A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban kasa shawara kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar ranar Juma’a, Shugaba Tinubu ya ce rayuwar kowane dan Najeriya tana da muhimmanci.

 

Ya ce bai kamata wani dan kasa ya rasa ransa a hannun gwamnati sakamakon sakaci, cin zarafi, rashin kulawa ko rashin bin ka’ida ba.

 

Shugaban ya kuma bayar da umarnin cewa idan bincike ya gano wani jami’in gwamnati ya taimaka wajen haddasa mutuwar mutanen ta hanyar aiki, cin zarafi ko sakaci, a kama shi sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!