Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawar sasanci da Twitter

Published

on

Gwamnatin tarayya ta fara tattaunawa da kamfanin sada zumunta na Twitter akan dakatar da harkokin kamfanin a Najeriya.

Rahoton jaridar The Nation, Ministan yada labarai Alhaji Lai Muhammad dake jagorantar manyan jami’an gwamnatin tarayya na shirin tattaunawa da kamfanin don dawowa cigaba da harkokinsa.

Rahoton ya ce wani babban hadimi na shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya tabbatar wa da jaridar cewa tuni an gama tsara yadda zaman zai gudana tsakanin bangarorin biyu.

A baya dai gwamnatin tarayya ta dakatar da Kamfanin na Twitter, a ranar 4 ga watan Yuli, sakamakon goge kalaman shugaba Buhari, da kamfanin yayi daga shafin sa da suka ce ya sabawa ka’idojin su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!