Labarai
Gwamnatin tarayya ta gargadi yan Najeriya kan shinkafar da ake shugo da ita
Gwamnatin tarayya ta yi gargadin cewa mafi yawa daga cikin shinkafar da ake shigowa da ita daga kasashen ketare tana da illa ga jikin bil adama.
Ministan yada labarai da raya al’adu Alhaji Lai Muhammed ne ya bayyana haka yayin wani taron manema labarai a garin Oro da ke yankin karamar hukumar Ifelodun a jihar Kwara.
Ya ce akwai bayanan da suka samu cewa yawancin shinkafar an noma ne domin amfanin dabbobi amma abin takaici wasu marasa kishin kasa ke safarar su zuwa cikin kasar nan su sayarwa jama’a.
Alhaji Lai Muhammed ya ce gwamnati ta sanya tsastsauran tsaro akan iyakokin kasar nan don kula da wadanda ke safarar irin wadannan shinkafa.
A cewar sa gwamnatin tarayya na aiki ba dare ba rana don ganin cewa kasar nan ta rika iya samar da isasshen shinkafa da zai biya bukatun al’ummar ta.