Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta koma tibirin sulhu da kungiyar malaman Jami’o’i
A yau ne gwamnatin tarraya ta koma kan tibirin sulhu da shugabannin kungiyar malaman jami’o’I ta kasa ASUU don warware bukatun kungiyar da ya kai ga har ta tsunduma yajin aikin sai baba ta gani.
A yayin makamancin taron da gwamnati ta yi da kungiyar ta ASUU a ranar 7 ga wannan watan da muke ciki, ministan kwadago Dr, Chris Ngige ya sanar da cewa, gwamnati ta fitar da fiye da Naira biliyan 15 don biya gibin albashin malaman, wanda yana da ga cikin babban batun da ya sanya malaman suka shiga yajin aikin.
Kusan makwanni 2 ke nan da gudnar da wancan taron da kuma sanar da fitar da kudin, amma kawo yanzu malaman sun cigaba da yajin aikin da suke ciki duk da cewar shugaban kungiyar malaman ta kasa ya ce kungiyar a zata ce unfan har sai kwamitin gudanarwar kungiyar yayi nazari kan batun tare da yanke shawarar kan sabon cigaban da aka samu da kuma matakin na gwamnatin tarayya kafin ta janye yajin aikin da ta shiga.