Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje sun gargadin da a guji labarun bogi a lokacin zabe

Published

on

Kungiyar ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje ta gargadi ‘yan Najeriya da su guji kitsa labarum bogi da kuma furta kalaman batanci da zai tunzura al’umma wajen tada rikici, kafin da yayin da kuma bayan babban zabe dake tafe.

Wannan na kunshe cikin sanarwar hadin gwiwa ta bayan taro da kungiyar ta fitar karkashin gamayyar jam’iyyun siyasa na kasar nan da kuma na tarayyar Turai  suka fitar

Sanarwar bayan taron ,ao dauke da sa hannun shugaban ta Mr Keneth Gbandi da wakilan jam’iyyu daban-daban da kuma wakilan kungiyoyin kishin al’umma da suka gudanar a can kasar Jamus yayin da suka aikewa kamfanin dilancin labaru na kasa NAN dake Abuja.

Kungiyar ta kuma yi kira ga ‘yan Najeriya da su hada kan su wuri guda da wanzar da zaman lafiya ba tare nuna bambacin adani ko siyasa ko kuma aladu ba, ta yadda za’a dakile furta kalaman batanci da kuma tada rikici a cikin al’umma.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!