Connect with us

Labarai

Gwamnatin Tarayya ta musanta cewa ta na shirin rushe Hukumar NBAIS

Published

on

Gwamnatin Tarayya ta musanta rade-radin da ke cewa tana shirin soke Hukumar Shirya Jarabawar Larabci da Addinin Musulunci ta Kasa NBAIS.

Hakan na cikin sanarwar da Daraktar Yaɗa Labaran Ma’aikatar Ilimi ta kasa, Boriowo Folasade, ta fitar a Daren jiya Talata.

Sanarwar ta ce rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da sauran wurare cewa Gwamnatin Tarayya da Majalisar Tarayya na nazarin soke NBAIS karya ne kuma ba su da tushe.

Ma’aikatar ta bayyana cewa ba ta gabatar da wani kudiri ga Majalisar Tarayya domin soke NBAIS ba, kuma ba ta kirkiri ko goyi bayan wata manufa da za ta kawo karshen hukumar ko rage mata ikon da doka ta ba ta ba.

Sanarwar ta ce NBAIS na ci gaba da kasancewa hukumar da gwamnatin tarayya ta amince da ita a tsarin ilimi, tare da tabbatar da cewa gwamnatin za ta ci gaba da tallafawa cibiyoyin ilimi da hukumomin shirya jarabawa da doka ta tanada.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!