Connect with us

Labarai

Majalisar Wakilai ta fara nazarin ƙudurorin sake fasalin rundunar soji

Published

on

Majalisar Wakilan Najeriya ta fara nazarin jerin ƙudurorin dokoki da ke da nufin sake fasalin tsarin rundunar soji da inganta walwalar jami’ai da tsofaffin sojoji, tare da ƙarfafa ƙarfin rundunar wajen fuskantar sabbin barazanar tsaro.

 

Da yake jawabi a taron sauraron ra’ayoyin jama’a na kwanaki biyu da Kwamitin Tsaro na Majalisar ya shirya a Abuja, Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya ce kudurorin na da muhimmanci wajen daidaita dokokin soja da sauye-sauyen da ke faruwa a fannin tsaro.

 

Ya bayyana cewa sabbin ƙalubalen tsaro da suka haɗa da fashin teku a yankin Gulf of Guinea, yaƙin yanar gizo da kuma haɗin gwiwar ƙungiyoyin ta’addanci da masu aikata manyan laifuka sun nuna buƙatar yin garambawul ga dokokin rundunar sojin Najeriya.

 

Daga cikin muhimman kudurorin da ake dubawa akwai kudirin Armed Forces Farms and Ranches Scheme Bill, wanda ke da nufin haɗa shirye-shiryen samar da abinci da ayyukan soja, musamman a yankunan da rikice-rikice suka shafa.

 

A nasa jawabin, shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Wakilai, Babajimi Benson, ya ce taron wata muhimmiyar dama ce ga masu ruwa da tsaki su taimaka wajen tsara dokokin da za su ƙarfafa tsaro, ilimin soja, bincike, kula da lafiya, walwalar tsofaffin sojoji, samar da abinci da kuma daidaito a rundunar sojin kasar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!