Labarai
Kebbi: Sojoji sun ƙwato tarin manyan makamai daga hannun ƴan bindiga

Dakarun Sojin kasar nan na Fansan Yamma da ke aiki a Jihar Kebbi, sun kwato tarin manyan makamai da kuma bama-bamai a ci gaba da ƙoƙari da nufin kawar da ta’addanci da sauran ayyukan miyagun laifuka a yankin Arewa maso Yamma.
Rahotonni sun bayyana cewa, an gudanar da wannan farmakin ne a yankin Dogon Daji da ke Ƙaramar Hukumar Dandi ta jihar, da ya yayin farmakin, jaruman dakarun sun yi amfani da ƙarfi wajen murƙushe ƙungiyar ‘yan ta’addan Lakurawa, lamarin da ya tilasta musu tserewa daga wajen.
A ci gaba da bin sawun ‘yan ta’addan da suka gudu ya kai ga gano da kwato dimbin makamai, bama-bamai da kayan aiki da suka bari a baya yayin tserewar su.
Mai magana da yawun rundunar, Laftanar Kanal Olaniyi Osoba, ya ce, kayan da aka kwato daga sansanin ‘yan ta’addan sun haɗa da bututun harba roka RPG da makaman rokokin yaƙi da dama da ake sama bututun harba roka da bama-bamai na gida masu yawa sai babura guda biyu da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen kai hari da caja ta batura, da wasu sauran kayayyaki.
Ya kuma ce, rundunar Sojin kasar nan za ta ci gaba da matsa lamba kan wadannan miyagun, tare da hana su damar gudanar da ayyukan su domin tabbatar da tsaro da lafiyar al’umma masu bin doka.
You must be logged in to post a comment Login