Labarai
Gwamnatin tarayya ta sanar da sabbin ka’idojin bude makarantu
Yayin da dama daga makarantun kasar nan za su bude a ranar litinin na makon gobe, gwamnatin tarayya ta kara fitar da wasu sabbin ka’idoji da ta zayyanawa makarantu domin kare dalibai daga kamuwa da cutar corona.
Cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ce ta bayyana haka yayin zantawa da jaridar PUNCH.
A cewar cibiyar ta NCDC wajibi ne makarantun su rika auna hatsarin da cutar corona ke da shi a duk mako don rage hatsarin da dalibai da malamai za su shiga.
Haka zalika an kuma bukaci jihohi da kananan hukumomi da su rika nazartar halin da cutar ke ciki a duk wata ko bayan watanni hudu-hudu.
Shugaban cibiyar dakile yaduwar cututtuka ta kasar Dr Chikwe Ihekweazu ya shaidawa jaridar cewa, wadannan mataki wajibi ne makarantu su rika daukarsu don kare lafiyar dalibai da malamai.
You must be logged in to post a comment Login