Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya ta shaidawa ma’aikatan lafiya muradinsu ba mai yiwuwa bane
Gwamnatin tarayya ta shaidawa ma’aikatan lafiya da ke tsaka da yajin aiki a yanzu haka cewa muradinsu na ganin an biyasu albashi daidai da Likitoci ba abu ne mai yiwuwa ba.
Ministan Lafiya Farfesa Isaac Adewole ne ya sanar da hakan a jiya Lahadi, cikin wata sanarwa mai kunshe da sa-hannun mataimakin daraktan yada labaran ma’aikatan Olajide Oshundum, lokacin da ya ke maida martani dangane da yajin aikin da kungiyar JUHESU ke ci gaba da yi.
Ya kara da cewa gwamnati na iya kokarinta wajen ganin an samu didaito kan wannan al’amari na yajin aikin ta hanyar tattaunawa da kungiyar ta JUHESU, inda ko a ranar 25 ga watan Afrilun nan da mu ke ciki a Ofishin Ministtan Kwadago da samar da aikin yi a Abuja.
Farfes Adewole ya bayyana cewa a cikin watan Satumban bara ne JUHESU ta mikawa gwamnatin tarayya bukatunta 15 da take muradin a duba, inda aka amince da 14 sannan ake ci gaba da tattauna yadda za samu daidaito a guda dayan da ya rage.
Har ila yau ya ce zancen yarjejeniyar da JUHESU ke gabatarwa a matsayin wadd aka cimma a shekarar 2014 ba haka batun yake ba, face kunshin bayanan yadda tattaunawarsu ta gudana da wasu bangarorin gwamnati.
A yau ne dai ake sa-ran za a koma kan teburin sulhu tsakanin bangarorin biyu don lalubo bakin zaren.