Labarai
Gwamnatin tarayya ta shiga ganawar sirri da NLC
Gwamnatin tarayya ta shiga ganawar sirri don sasantawa tsakanin ta da kungiyar kwadago ta kasa.
Ministan kwadago da nagartar aiki Dr, Chris Ngige ne ya jagoranci bangaren zartarwar da aka fara a dazun a babban birnin tarayya Abuja.
A dai kwanakin baya ne kungiyar kwadagi ta kasa ta baiwa gwamnatin tarayya wa’adin da ta fara biyan ma’aikata da sabon tsarin mafi karancin albashi, bayan da shugaban kasa Muhamadu Buhari ya sanya hannu kan dokar sabon albashin tun a ranar 18 ga watan Afirilun da ya gabata.
Rahotanni sun bayyana cewar, taron yana cikin jerin ganawar da shugabanin kwadago suka yi don aiwatar da sabon mafi karancin albashin na Naira dubu talatin 30.
Majalisar dattijai Najeriya ta roki kungiyar kwadago dakatar da yajin aikin da suke yunkurin shiga
Ma’aikatan jihar Adamawa sun yi zanga-zanga kan kin biyan albashi
Shugaba Buhari ya taya shugaban kungiyar kwadago murna lashe zabe
A dai shekaran jiya ne kungiyar kwadago ta kasa ta raba takardar bayan taro, tana mai gargadin cewa in har gwamnati bata dauki mataki ba, to babu shakka kungiyar zata tsunduma yajin aiki a ranar 16 ga wannan watan na Okotoba.
Wanna na kunshe cikin sanarwar babban sakatare na kungiyar JNPSNC Mr, Alade Lawal ya fitar cewa an fara taron ne ya sami halatar daukacin jagororin gamayyar kungiyoyi ta kasa.