Kasuwanci
Gwamnatin tarayya ta tabbatar da Rasuwar mutane 13 masu hakar ma’adinai a Zamfara

Gwamnatin tarayya, ta tabbatar da Rasuwar mutane 13 daga cikin 15 masu hakar ma’adinai da suka makale a wani rami mai zurfi a kauyen Jabaka da ke kamar hukumar Maru a jihar Zamfara.
Hakan na cikin wata Sanarwa da mataimaki na musamman kan harkokin yada labarai ga Ministan bunkasa harkokin ma’adanai Segun Tomori, ya fitar a birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta ruwaito cewa, Ministan bunkasa harkokin ma’adanai Dakta Dele Alake, ya bayar da umarnin tura jami’an ma’adinai da za su jagoranci aikin ceto tare da hadin gwiwar jami’an gwamnatin jihar ta Zamfara.
You must be logged in to post a comment Login