Labarai
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kalaman Theophilus Danjuma
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da kalaman da tsohon Ministan tsaro Theophilus Danjuma ya furta cewa jami’an tsaron kasar nan na cewa su na hada kai da yan ta’adda wajen gudanar da ayyukan ta’addaci a kasar nan.
Wanan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai Magana da yawun Ministan tsaron Kasar nan Kanal Tukur Gusau ya fitar, inda ya ce kalaman na Janar Danjuma kalamai ne na tunzura al’umma daya kamata duk wani dan kasa na gari yayi watsi da su.
Haka itama rundunar sojin kasar nan ta fitar da wata sanarwar da safiyar yau Lahadi inda ta bayyana kalaman na Janar Danjuma a matsayin rashin adalci da kuma abin mamaki da ya zo a wanan lokacin da rundunar soji ke iya kokarin ta wajen ganin ta magance al’amura.
A ranar Asabar din da ta gabata, Janar Danjuma dai ya zargi jami’an tsaron kasar nan da hada baki da yan ta’adda wajen kashe wadanda basu ji ba ba su gani ba, a cewar sa ana kashe al’ummar kasar nan kusan a kowacce rana, amma jami’an tsaro basa wani yunkurin na dakatar da al’amarin sabo da suna da hannu dumu-dumu a cikin al’amarin.
A cewer Danjuma yan zu lokacin yayi da al’ummar kasar nan za su dauki matakin kare kansu da ga hannun yan ta’addan tun da dai jami’an tsaron ba za su iya ba.