Manyan Labarai
Gwamnatin tarayya ta yi yarjejeniya da shirin Sasakawa akan noma
Gwamnatin tarayya ta sanya hannu kan yarjejeniya tsakaninta da kungiyar Sasakawa ta Afrika domin magance matsalar asarar albarakar noma da mafi yawan manoma ke fuskanta.
Ministan noma da raya karkara Alh Sabo Nanono ne ya bayyana haka ga manema labarai a wata takarda da daraktan yada labarai na ma’aikatar noma Mr Theodore Ogaziechi.
Ministan ya kara da cewa yarjejeniyar da gwawmantin tarayya ta shigar tsakaninta da Sasakawa wani yunkuri ne na ingantawa tare da taimakawa manoma wajen cin ribar abinda suka shuka da amfani da hanyoyin cigaban zamani don noman su.
Ya ce zai taimaka wajen sayar da albarka noma cikin sauki ga manoma, tare da baiwa matasa da mata damar shiga sana’ar noma , da samar da wadataccen abinci kamar yadda yake a manufofin majalisar dinkin Duniya.
Ministan dai ya sha alwashin marawa shirin Sasakawa a nan Najeriya , wanda yace yana daga cikin manofofin Shugaba Buhari na na tabbatar da abinci ya wadata tare da bunkasa tattalin arzikin Najeriya a waadin mulkinsa na biyu.
Da yake magana shugaban gidauniyar NIPPON Mr Ichiro Kabasawa ya ce gidauniyar sa zata taimaka wajen habaka harkar noma.
NIPPON dai wata gidauniya ce ta kasar Japan da take taimakawa da kudade ga cibiyoyin noma irin su Sasakawa don inganta noma.