Labarai
Gwamnatin Tarayya za ta dauki ma’aikatan lafiya 150

Gwamnatin Tarayya ta amince da daukar sabbin ma’aikatan lafiya 150 domin aiki a asibitocin gidajen gyaran hali a fadin kasar nan. Wannan ya hada da likitoci 50 da kuma jinya 100 domin inganta kula da lafiyar fursunoni.
Ministan harkokin cikin gida na Najeriya, Olubunmi Tunji-Ojo, ne ya bayyana hakan a Abuja lokacin da Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idris, ya kai masa ziyarar ban girma. Ya ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ne ya amince da daukar ma’aikatan bayan an lura da karancin ma’aikatan lafiya a wasu gidajen gyaran hali.
Ministan ya ce wasu cibiyoyin gyaran hali ba su da likitoci kwata-kwata, inda ya bada misalin wata cibiyar da ke jihar Rivers. Ya kuma kara da cewa wasu asibitocin gidajen gyaran hali, ciki har da na Kuje, suna da kayan aikin da za su iya yin manyan tiyata, tare da jaddada cewa gwamnati na kokarin inganta rayuwar fursunoni da kuma horas da su sana’o’i.
You must be logged in to post a comment Login