Labarai
Gwamnatin tarayya zata kashe naira biliyon goma wajen sayen maganin Kwari
Gwamnatin tarayya za ta kashe naira biliyan goma sha uku don sayan maganin Kwari da za ayi feshi da shi a daminar bana.
Ministan gona Muhammed Sabo Nanono ne ya bayyana haka yayin kaddamar da fara feshin maganin kwari na bana a jihar Kebbi.
Buhari ya rabawa manoma irin shuka a Kano
Buhari ya ce nan ba da dadewaba za’a komawa makarantu
Ya ce, gwamnati ta dauki wannan mataki ne don yin rigakafi musamman ganin cewa, an samu labarin bullar wasu tsunsaye jam baki da ke cinye amfanin gona a yankin gabas ta tsakiya da kuma gabashin afirka.
Alhaji Sabo Nanono ya kara da , dukkannin jihohin da ke kan iyakokin kasar nan gwamnati za ta kara sanya ido akansu don ganin tsuntsayen ba su yi barna ga manoma a kasar nan ba.
You must be logged in to post a comment Login