Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya zata tallata takardun lamuni na kimanin fiye da naira biliyan arba’in da takwas
Gwamnatin tarayya za ta tallata takardun lamuni da darajar su ta kai naira biliyan arba’in da takwas da miliyan dari shida sannan ta biya takardun lamunin naira biliyan casa’in da daya a cikin makon nan.
A cewar babban bankin kasa CBN manunfar fitar da takardun lamunin shine domin daidaita hada-hadar tattalin arzikin kasar nan.
Ko a makon jiya ma babban bankin kasa CBN ya sayar da takardun lamunin da darajar sa ya kai naira biliyan dari uku da hamsin wadanda aka tallata su kuma an gudanar da su ne a matakan hada-hada na takaitaccen zango da kuma matsakaicin zango.