Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Majalisa a Nijeriya ta fara bincike kan badakalar biliya 81 ga wasu Jihohi 10

Published

on

Majalisar dattijai

Kwamitin majalisar wakilan Najeriya mai bincike a kan yadda aka yi amfani da asusun raya muhalli da alkinta yanayi da wasu kuɗaɗen asusun da ya shafi shirin dashen itatuwa da aka fi sani da Great Green Wall Project, ya soma binciken hukumar da ke lura da shirin kan yadda ake zargin ta kashe naira biliyan 81 domin dashen bishiyoyi miliyan ashirin da ɗaya a jahohin arewa da ke kan iyakar Najeriya

Jihohin sun haɗa da Kebbi da Sokoto da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Bauci da Gombe da Adamawa da Yobe da kuma Borno.

Daraktan Hukumar ta NAGWW, Yusuf Maina Bukar, ya shaidawa kwamitin cewa ‘hukumar ta kashe naira miliyan 697.71 wajen gyara ofishinta da kuma naira biliyan 11.28 wajen gudanar da manyan ayyuka’.
Ya ƙara da cewa ‘galibin kuɗaɗen da hukumar ke samu sun fito ne daga cikin kashi 15 cikin ɗari na kuɗaɗen asusun alkinta yanayi da muhalli da kuma waɗanda gwamnatin tarayya ke samarwa.

Baya ga wannan ma kwamitin ya kuma binciki Babban Bankin Najeriya game da wasu asusun ajiya fiye da bakwai da bankin ya san da su.

Wasu takardun bayanai masu shafuka shida ɗauke da kwanan watan 22 ga watan Agustan 2023 da bankin na CBN ya miƙawa kwamitin sun nuna cewa an sakawa asusun hukumar kimanin naira 9,465,960,382.57 tun daga 2015 zuwa wannan ranar.

Babban akanta janar na Najeriya, Oluwatoyin Madein ya bayyana cewa Hukumar da ke lura da shirin dashen itatuwa da alkinta yanayi ta NAGWW ɗin ta ƙarbi kuɗin da yawan sa ya kai naira 19,377,726,506.95 tun daga watan Febrairun 2019 kawo yanzu

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!