Kiwon Lafiya
Gwamnatin tarayya zata tattauna da kungiyar kwadago don dakile barazanar shiga yajin aiki
Gwamnatin tarayya ta ce manufar kiran taron tattaunawa da kungiyoyin kwadago da za a yi a gobe juma’a shi ne domin, domn dakile barazanar shiga yajin aikin da kungiyoyin suka yi kan batun mafi karancin albashi na naira dubu 30.
Sai dai shugabanin gamayyar kungiyoyin kwadagon sun ce a yanzu kam sun wuce loacin da za a yi ta kiran taron tattaunawa a binda suke bukata shi ne kawai a aike da kudirin gaban majalisun kasar nan.
Gwamnatin tarayya ce dai karkashin ministan kwadago Chris Ngige ne suka aike da takardar gayyatar ga kungiyoyin kwadagon domin tattauanwa a ranar juma’a mai zuwa.
Cikin wata sanarwa da daraktan yada labaran ma’aiaktar Olowookere ya fitar jya a Abuja da ta bukaci gamayyar kungiyoyin kwadagon su taimaka sub a da hadin kai su kuma halarci zaman.