Labaran Wasanni
Gwamnatin tarayya zata yiwa kungiyoyin kwallon kafa lasisi – Minista
Ministan matasa da wasanni, Sunday Dare, ya ce, matakin da gwamnatin tarayya ta dauka na mayar da wasanni daga harkokin nishadantuwa zuwa kasuwanci, ya sanya dole a yiwa kungiyoyin kwallon kafar kasar nan lasisi.
Sunday Dare ya bayyana haka ne a shafin sa na Twitter, inda ya ce, ma’aikatar wasanni za ta tabbatar da ta yi wa kungiyoyin kwallon kafa na cikin gida lasisi.
Ya kuma ce, hakan na dai-dai da bukatar shugaban kasa Muhammadu Buhari ta sauya salon harkokin wasanni zuwa wani bangare na harkokin kasuwanci.
Babban sakataren ma’aikatar wasanni, Gabriel Aduda, ya ce, ba za’a dawo ci gaba da harkokin wasanni ba musamman gasar League ta kasa, har sai an tabbatar da kowace kungiya ta samu lasisin ta.
Aduda ya kara da cewa, minista Sunday Dare ya umarci hukumar kwallon kafa ta kasa da ta tattauna da kungiyoyin tare da bukatar yin biyayya ga ka’idojin tafikar da kudade kafin a saka ranar dawowa ci gaba da gasar cin kofin kwararru ta kasa.
Haka zalika, Dare ya ce yi wa kungiyoyin lasisi zai taimaka sosai wajen ganin kowace kungiya ta cika ka’idoji da tsarin gudanarwa na shekara-shekara, duba da yadda wasu daga cikin kongiyoyin ke gaza biyan ‘yan wasa da ma’aikanta su albashi tsawon watanni da dama.
You must be logged in to post a comment Login