Labaran Wasanni
Michy Batshuayi zai tsawaita kwantiragin sa da Chelsea
![](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2020/09/NINTCHDBPICT000546772122.jpg)
Dan wasan gaban kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Michy Batshuayi, zai saka hannu domin tsawaita kwantiragin sa da kungiyar kafin ya tafi Crystal Palace a matsayin aro.
Dan wasan, mai shekaru 26, kwantiragin na sa zai kare a karshen kakar wasanni mai zuwa, yayin da tsawaita kwantiragin zai hana dan wasan tafiya a matsayin kyauta.
A dai tsakiyar kakar wasa ta shekarar 2018 zuwa 2019 ne dan wasan ya je Crystal Palace a matsayin aro, inda ya jefa kwallaye 6 a wasanni 13.
You must be logged in to post a comment Login