Labarai
Gwamnatin Yobe ta rufe dukkannin makarantun kwanan jihar
Gwamnatin jihar Yobe ta sanar da rufe makarantun kwana a jihar a wani mataki na kare dalibai sakamakon yawaitar sace daliban da ‘yan bindiga ke yi a jihohin arewacin kasar nan.
Kwamishinan ilimin jihar Dr. Muhammed Idris ne ya bayyana haka a lokacin da ya ke ganawa da manema Labarai a Damaturu babban birnin jihar.
‘‘Mun bada umarnin rufe dukkannin makarantun sakandire ne don kare lafiyar daliban’’ a cewar Kwamishinan.
Kwamishinan ya kara da cewa, ma’aikatar ilimin za ta yi aiki da hukumomin tsaro da ke jihar don tabbatar da cewa an bada tsaron da ya dace a makarantun kafin komawar daliban.
You must be logged in to post a comment Login