Labarai
Gwamnatocin jihohi ne za su rinka ciyar da daurarru- Minista
Gwamnatin tarayya ta ce, daga yanzu gwamnatocin jihohi ne za su rika ciyar da fursunoni da ke gidajen ajiya da gyaran hali.
Ministan harkokin cikin gida Rauf Aregbesola ne ya sanar da hakan, lokacin da yake jawabi a wajen wani babban taro na kwanaki 2 kan rage cunkoson Fursunoni a gidajen gyaran hali da aka gudanar a Birnin tarayya Abuja.
Ya ce, ‘hakan ya biyo bayan gyare-gyaren da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan a baya-bayan nan wanda Ya nuna cewa, a yanzu an baiwa jihohi ikon ciyar da fursunonin da ke daure’.
Aregbisola ya kuma ce, ‘duk jihar da ta gaza ciyar da fursunoninta, to kuwa dole ne ta biya gwamnatin tarayya kudin ciyarwar’.
Idan za a iya tunawa, a baya gwamnatin tarayya ta ware sama da naira biliyan 22 domin ciyar da fursunoni a dukkanin gidajen gyaran hali guda 244 da ke fadin Nigeriya.
You must be logged in to post a comment Login