Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Sarkin Karaye ya nada Alhaji Umar Musa Kwankwaso a matsayin sabon Majidadi

Published

on

Mai martaba sarkin Karaye Dakta Ibrahim Abubakar II, ya nada Alhaji Umar Musa Kwankwaso a matsayin sabon Majidadin Karaye.

Sanarwar nadin na kunshe cikin wata wasika mai dauke da sa hannun jami’in yada labarai na masarautar, Haruna Gunduwawa ya fitar.

Sanarwar ta ce, za a yi bikin nadin nasa ne tare da wasu mutane 11 da sarkin ya nada su sarauta a ranakun 19 da 26 ga wannan watan da muke ciki na Mayu.

Alhaji Umar Musa Kwankwaso dai, dan uwa ne ga tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP a zaben da ya gabata Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!