Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya Pele ya mutu yana da shekaru 82

Published

on

Fitaccen gwarzon dan kwallon kafa na duniya dan ksar Brazil, Edson Arantes do Nascimento Pele ya rasu yana da shekaru 82.

Pele ya rasu ne a ranar Alhamis 29 ga watan Disamba na shekarar 2022, bayan fama da rashin lafiya.

Ya rasu ne sakamakon fama da Cutar Daji ta Ƙaba (Colon Cancer ), da kuma cutar ƙoda.

A kwanakin baya dai an ta yada labarin karya cewa Pele ya rasu.

Ana ganin dai Pele shi ne dan wasan da ba a taba samun irin sa ba a tarihin duniya, ya kuma lashe gasar cin kofin duniya sau uku yana cin ga kasar Brazil, a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1970.

Ya kuma zura kwallaye 1,281 a raga a wasanni 1,363 da ya buga.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!