Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Ƙetare

Djokovic ya kai wasan karshe a gasar Australian open

Published

on

Zakaran gasar Garnad Slam har sau tara, Novak Djokovic yav kai wasan karshe a gasar Austaralian Open, bayan doke Tommy Paul dan kasar Amurka.

Dan kasar Sabiya, Djokovic, mai shekaru 35, ya samu nasara kan dan kasar Amurkan Paul da ci 7-5 6-1 6-2.

A hannu guda kuma shima dan wasan kasar Girka Stefanos Tsitsipas mai shekaru 24, ya kai wasan karshen a karon farko a gasar ta Grand Slam, bayan nasara da yayi kan Karen Khachanov.

Tsitsipas dake matakin lamba uku a Duniya ya doke dan kasar Rashan da ci 7-6 (7-2) 6-4 6-7 (6-8) 6-3.

‘Yan wasan biyu sun kara a wasan karshe a shekarar 2021 a gasar French Open, inda Djokovic din yayi nasara kan Tstsipas, wanda dama ce ga dan kasar Girkan ya rama abinda dan kasar Sabiyan yayi masa.

Haka zalika duk wanda ya samu nasara a cikin su a wasan karshen shi ne zai zama lamba daya a Duniya.

Rahoton: Sunusi Shu’aibu Musa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!