Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Qatar 2022: Morocco ta karya tarihin shekararu 24 bayan lallasa Belgium

Published

on

Tawagar kwallon ƙafa ta ƙasar Morocco a karon farko bayan shekaru 24, ta sami nasara a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2022 da ake gudanarwa a ƙasar Qatar.

Morocco dai ta sami nasarar ne bayan da ta doke ƙasar Belgium da ci 2 da nema a wasa na biyu a rukuni na shida a ranar Lahadi.

A minti na 73 Morocco ta zura ƙwallon farko ta hannun Abdelhamid Sabiri, sannan Zakaria Aboukhlal ya ƙara ta biyu daf da lokaci zai cika.

Da wannan sakamakon Morocco ta haɗa maki huɗu kuma ta hau kan Belgium mai maki uku a rukunin na shida.

Rabonda tawagar ta Atlas Lions ta sami irin wanan nasara tun a shekarar 1998 a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a ƙasar Faransa, inda ta casa ƙasar Scotland da ci 3 babu ko ɗaya.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!