Kiwon Lafiya
Gwmnatin jihar Zamfara ta bada tallafin naira miliyan 8 ga sojojin Nijar da suka rasa rayukansu
Gwamnatin jihar Zamfara ta baiwa iyalan sojojin Nijar da suka rasa rayukan su sakamakon kwantan baunar da aka yi musu a dajin Dumburum da ke karamar hukumar zurmi tallafin naira miliyan takwas da dubu dari biyar,
Rahotannin sun yi nuni da cewa sojojin sun rasa ransu ne a dajin lokacin da suke aikin kwantar da tarzoma tare da sojin Najeriya, har ma yayin kwantan baunar sojin Najeriya biyar suka rasa ransu.
Gwamnan jihar ta Zamfara Abdul’azez Yari ne ya bayar da tallafin da kan sa bayan da ya ziyar ci kasar ta Nijar a jiya litinin domin ta’aziyyar sojojin da aka rasa a jihar ta Zamfara.
A cewar gwamna yari ko wane soja da ya rasa ransa iyalan sa za su amfana da naira miliyan daya yayin da wadanda suka samu raunuka kuma za a basu naira dubu dari biyar.
Gwamna yarin ya samu tarbar ministan tsaron kasar ta Nijar Alhaji Kalla Kukhtari, sai kuma Gwamnan jihar Maradi Alhaji Zakiri Umar da kuma wasu jami’an gwamnatin kasar ta Nijar.