Coronavirus
Gyaran kasafin kudi ba zai shafi bangaren cimaka ba –Inji gwamnatin Jigawa
Ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare ta jihar Jigawa tace kasafin kudin da aka warewa bangaren cimaka (Nutrition) baichanza ba daga yanda aka ware masa tun asali.
Babban sakataren ma’aikatar Alhasan Ibrahim Market ne ya bayyana hakan a lokacin da kungioyin ayyukan ‘yan majalisu da cigaba ta CISLAC da kungiyar ‘yan jaridu masu kula da ayyukan lafiya ISMPH, karkashin gidauniyar Aisha Buhari suka kai ziyar kan batun kasafin kudin cimaka a ofishinsa a ranar Talata 17 ga watan Yunin 2020.
Ibrahim yace kasafin kudin al’amuran cimaka yakai kimanin Naira Miliyan 450 Wanda ya sha ban-ban da na shekarar bara.
A satin daya gabata ne gwamnatin jihar Jigawa ta rage kasafin kudin jihar da kimanin kaso Ashirin 20 cikin dari sakamakon annobar COVID-19.
A jawabinsa Ko-odinetan kungiyar CISLAC na jihar Jigawa Wanda ya jagoranchi tawagar, Kwamaret Muhammad Musbahu Basirka, ya bayyana irin gudunmawar da kungiyoyin ke bayarwa a matsayin wani cigaba musamman a bangaren lafiyar yara da mata masu juna biyu.
Daga karshe Basirka ya godewa kungiyoyin hadi da Babban sakataren ma’aikatar kasafin kudi da tsare-tsare na jihar Jigawa Alhasan Ibrahim Marke, wajen tabbatar da cigaban jihar.
You must be logged in to post a comment Login